Abin da ya sa mata suke daina fim idan sun yi aure

Da dama daga cikin matan da ke fitowa a fina-finan Kannywood na daina fim da zarar sun yi aure ko da kuwa suna tsaka da tashe.

Yayin da wasu ke cewa ba za su hada fim da aure ba, wasu kuwa cewa suke yi babu abin da zai hana su hada biyun.

Jarumar fina-finan Hausa Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso ta ce mijinta ya barta ta ringa fitowa a fina-finan Hausa duk da tana da aure saboda mijinta wayayye ne kuma mai ilimi.

Jarumar tana daya daga cikin yan matan masana’antar Kannywood da zasu ajiye yin fim da zaran sunyi aure domin mayar da hankali wajen kula da iyali

Hirar ta da wakilin BBC Hannatu tana mai cewa
“Ko wace mace tana son ta ganta a gidanta kuma tana kula da iyalen ta. Idan ina da mijin yanzu idan nayi aure, ka gan zan fita da safe zuwa wajen aiki wa zai kula dashi? Idan kuma na fara tara yaya wa zai kula mun dasu?.
Ka gan ya zama dole in hakura da daya. Kuma harkar fim dinmu ba a iya kano kadai muke yi muna iya zuwa wasu garuruwa muyi.
Ina da miji zai barni in tafi wani gari inje inyi kwana biyar zuwa goma wajen daukar fim? kaga abu ne mai kamar wuya.
“Ni daia zaman aure ya fiye mun kudin da zan samu kuma ya fiye mun komai da komai ma” .

Share this:

Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *