Buhari ya tafi New york domin halartar taron majalisar dinkin duniya

A taron majalisar shugaban zai yi magana game da abubuwan dake faruwa a kasar Nigeria

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja a safiyar yau domin halartar taron majalisar dinkin duniya a birnin New york.

A bisa labarin da channels Tv ta fitar, shugaban ya bar garin Abuja a safiyar ranar lahadi 17 ga watan Satumba zuwa kasar Amurka.

Buhari ya bar kasa tare da wasu ministocin shi wadanda ba’a fitar da sunayen su.

A taron majalisar shugaban zai yi magana game da abubuwan dake faruwa a kasar Nigeria.

Taken taron majalisar na wannan shekarar shine;“mayar da hankalin kan muitane; neman zamn lafiya da samad da rayuwa managarci”.

Ana kyautata zaton cewa shugabamn zai kara magana akan yadda za’a mayar kudaden gwamnati da aka sata a kasar.

Share this:
Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *