Na Ji Dadi Sosai Da Na Fara Fitowa a Fina Finan Nollywood Inji Hadiza Gabon

Fitacciyar jarumar masana’antar kannywood Hadiza Aliyu Gabon zata bi sahun wasu shahararru dake masana’antar wajen fitowa a fina-finan Nollywood wanda ake yi a kudanci ƙasar.

Zata fito cikin sabon shirin fim wanda fitaccen dan wasan Nollywood Mike Ezuronye zai shirya mai suna ‘Lagos fake life’. Wannan shine karo a farko da jarumar zata fito cikin shirin Nollywood amma ba shirin farko bane wanda take turanci a ciki. “Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a wani gajeren fim na turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood” inji Hadiza.

Jaruma mai tauraro ta nuna farin ciki game da wannan damar na yin fim da wasu jiga-jigan yan wasan Nollywood.
Ta shaida ma BBChausa cewa ta amince da fitowa cikin shirin bisa ga ka’ida na cewa baza ta fito a matsayin da zai sabawa addini ko al’adar ta. A cewarta; “Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna ‘Lagos real fake life’ “Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da addini da al’adata ba”

Jarumar ta shaida cewa babu wani bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finai a kannywood da nollywood face bambancin harshe.

Share this:
Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *