Saboda albarkar Shehu Inyass aka yi ruwa jiya a Kaduna Inji wani ‘Dan ‘Darika

Mun samu labari cewa wani kasurgumin Mabiyin ‘Dan ‘Darika yayi ikirarin cewa saboda albarkar Sheikh Inyass ne aka samu ruwan sama a Garin Kaduna bayan an dade ana tsammanin saukan ruwan saman amma shiru.

Wannan Bawan Allah mai suna Jibril @Jaybee_am yayi amfani da shafin sa na Tuwita jiya inda yace an dade ana jiran ruwan sama a Kaduna bana ba a samu ba sai bayan da aka fara Mauludin ranar haihuwar Sheikh Inyass a jiya.

Jihar Kaduna dai na cikin Garuruwan da ba ayi ruwan sama ba a wannan shekarar duk da an samu saukar ruwan a Jihohin da ke Makwabtaka da Garin. Malam Jibril yace tabarrukin Shehin na ‘Darika ne ya sa ruwa ya sauka a jiya.

Idan ba ku manta ba a jiya ne ‘Yan darikar Tijjaniya su kayi bikin tunawa da babban Shehin su kuma babban Waliyyi Ibrahim Inyass wanda aka haifa a irin wannan lokaci. Ibrahim Inyass ya rasu ne dai shekaru fiye da 40 da su ka wuce.

Share this:

Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *